​Biden Ya Zabi Bakar Fata A Matsayin Sakataren Tsaron Amurka A Karon Farko

2020-12-08 15:00:55
​Biden Ya Zabi Bakar Fata A Matsayin Sakataren Tsaron Amurka A Karon Farko

Zababben shugaban kasar Amurka Joe Biden ya zabi bakar fata dan asalin Afirka a matsayin sakataren tsaron Amurka, wanda shi ne karon a tarihin Amurka da wani bakar fata zai rike wannan matsayi.

Jaridar Politico ta kasar Amurka ta bayar da rahoton cewa, Zababben shugaban kasar Amurka Joe Biden ya zabi bakar fata dan asalin Afirka Janar Lloyd Austin a matsayin sakataren tsaron Amurka, wanda ke nuni da canjin da aka samu a cikin tsarin rabon mukaman gwamnatia kasar.

Rahoton jaridar ya ce, kafin wannan lokacin an yi zaton cewa Michelle Flournoy ce Biden zai zaba domin rike wannan matsayi, wadda kuma ita ce dama aka yi niyar baiwa matsayin a zaben 2016, idan da Hillary Clinton ta samu nasarar zama shugabar kasa a lokacin.

Joe Biden ya yi alkawalin cewa ba zai tauye wa kowane bangare na al’ummar Amurka hakkinsa a cikin tsarin raba mukaman gwamnati ba, musamman bakaken fata da ya ce sun fuskanci matsananciyar wariya da kyama karkashin siyasar mulkin Donald Trump.

Ko a makon da ya gabata ma Joe Biden ya zabi wani dan Najeriya kuma haifaffen kasar ta Najeriya, wanda yake da takardun zama dan kasar Amurka a halin yanzu wato Adewale Adeyemo, a matsayin mataimaki na farko ga sakataren baitul mali na kasar Amurka.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!