​Najeriya: Shugaba Buhari Zai Bayyana A Gaban Majalisa

2020-12-08 14:57:45
​Najeriya: Shugaba Buhari Zai Bayyana A Gaban Majalisa

Shugaba Buhari na tarayyar Najeriya zai bayyana gaban majalisun dokokin kasar na dattawa da wakilai, domin yin bayani kan halin da ake ciki dangane da batun tsaro.

Majiyoyin fadar shugaban kasar ne suka sanar da hakan, cewa a ranar Alhamis mai zuwa shugaba Buhari zai bayyana a gaban majalisun kasar, inda zai yi bayani kan halin da ake cikin dangane da matakan da yake dauka na tabbatar da tsaro a kasar.

Wannan dai na zuwa bayan da majalisar wakilan kasar ta bukaci shugaba Buhari da ya bayyana a gabanta domin bayar da bayani kan matakan da yake dauka a bangaren tsaro, biyo bayan kisan na yankan rago da mayakan Boko Haram suka yi wa manoma a jihar Borno.

Majalisar ta yi wannan kiran ne bayan da ‘yan majalisar wakilai masu wakiltar jihar Borno suka gabar da daftarin kudiri kan hakan, wanda majalisar ta amince da shi.

Ita ma a nata bangaren majalisar dattawan Najeriya ta sake nanata kiranta ga shugaba Buhari, na ya sauke manyan hafsoshin tsaron kasar, saboda abin da majalisar ta kira gazawarsu wajen kasa tabbatar da tsaro a kasar.

Duk da cewa dai sanarwar fadar shugaban kasar ba ta yi bayani dalla-dalla kana bin da Buhari zai yi magana a kansa ba, amma dai bisa ga abin da majalisar ta bukata a takardar kiranye da ta aike masa, tana bukatar bayani ne kan matakan da yake dauka dangane da harkar tsaro da ke kara tabarbarewa a kasar.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!