An Soma Kidayar Kuri'un Zabe A Kasar Ghana

A Ghana, an fara kidayar kuri’un zaben shugaban kasa gami dana ‘yan majalisar dokoki a wasu mazabun kasar.
A jiya Litini ne dai aka jefa kuri’a a zaben shugaban kasar gami dana ‘yan majalisar dokoki.
‘Yan takara 11 ne da suka hada da mata uku ke fafatawa a zaben shugabancin kasar.
Manyan 'yan takara a zaben shugabancin kasar su ne Shugaba Nana Akuffo-Addo mai neman wa’adi na biyu da kuma babban abokin hamayyarsa tsohon Shugaban kasar, John Dramani Mahama.
Yanzu dai hankula sun karkata a sakamakon zaben da ake sa ran fitarwa nan da sa’o’I 24.
Rahotanni daga kasar dai sun ce an gudanar da zaben cikin lumana, saidai an fuskanci ‘yan matsaloli a wasu wuraren, inda wasu ‘yan bindga da ba’a tantance ko suwa ne ba suka bude wuta kan motar wasu mambobin jam’iyyar NDC mai adawa.
A wasu wuraren kuma an fusknaci dan tsaiko wajen bude runfunan
zabe kamar yadda tsara saboda rashin kayan aiki.
024