Siriya Da Iran Sun Sha Alwashin Karfafa Alakar Dake Tsakaninsu

2020-12-08 10:19:40
Siriya Da Iran Sun Sha Alwashin Karfafa Alakar Dake Tsakaninsu

Kasashen Siriya da Iran, sun sha alwashin karfafa alakar dake tsakaninsu, ta fuskar tattalin arziki da kuma yaki da ta’addanci.

Wannan bayanin na kunshe ne a sanarwar bayan taron da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka fitar, yayin ziyarar da ministan harkokin wajen Siriya ya kawo a Tehran.

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawwad Zarif, ya ce yana da kyau a rika samun irin wannan tattaunawa lokaci zuwa lokaci tsakani Iran da Siriya dama wasu kasashe.

A nashi bangare ministan harkokin wajen kasar ta Siriya, Faisal Mekdad, godewa Iran ya yi game da irin goyan bayan da take baiwa kasarsa kan yaki da ta’addanci da tsatsauran ra’ayi.

A daya bangaren ya kuma isar da sakon ta’aziyya na shugaban Bashar Al-Assad da al’ummar Siriya, game da kisan masanin nukiliyar kasar ta Iran Mohsen Fakhrizadeh.

M. Mekdad, ya kuma kalubalanci ayyukan Amurka a yankin wanda a cewarsa su ne ke kara rura wutar rikici a yankin.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!