Iran Ta Yi Kira Ga Kasashen Saudiyya Da Bahrain Da Su Rika Maganganu Daidai Da Matsayinsu

2020-12-07 19:48:08
Iran Ta Yi Kira Ga Kasashen Saudiyya Da Bahrain Da Su Rika Maganganu Daidai Da Matsayinsu

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Sa’id Khatib Zadeh wanda yake mayar da martani ga kasashen Saudiyya da Bahrain da suke nemi a shigar da su a cikin duk wata tattaunawa ta nan gaba akan shirin Nukiliya, da cewa; Ya kamata wadannan kasashen su rika yin Magana daidai da girmansu.

Sa’idzadeh ya kara da cewa; Wasu kasashen sun zubar da duk wani mutunci da suke da shi, domin su cimma manufofinsu a zamanin shugaban Amurka mai barin gado.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Wadannan kasashen sun kuma kashe makudan kudade domin su sami yardarm shugaban Amurka da ya fadi a zabe.

Har ila yau, ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta bakin kakakinta ta dorawa Saudiyya alhakin mawuyacin halin da Yemen take ciki na yunwa da yaki da zubar da jini.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!