Jami’an Tsaro A Birnin Ikko Suna Kokarin Hana Barkewar Wata Sabuwar Zanga-zangar Kin Jinin Ketar “Yansanda
2020-12-07 19:42:31

Rahotanni daga Nigeria sun ce an aike da ‘yan sanda dakuma sojoji zuwa yanki Lekki da ke birnin Ikko domin dakile yunkurin na sake farfado da Zanga-zangar nuna kin jinin ‘ketar ‘yan sandan SARS.
Jaridar Punch ta ambaci cewa; ta tuntubi
kakakin ‘yan sandan Ikko Muyiwa Adejobi da safiyar yau Litinin,amma ya ki mayar
da jawabi.
Tun a makon da ya gabata ne dai ‘yan
sanda da kuma sojoji su ka yi gargadin cewa; ba za su bari a sake farfado da
Zanga-zangar da aka yi ba ta neman rusa
rundunar ‘yan sanda ta SARS.
A gefe daya, shugaban kasar Nigeria, Muhammadu
Buhari ya yi gargadin cewa za a dauki mataki mai tsauri akan aikin bada da
sunan zanga-zangar.
013
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!