Majalisar Dokokin Kasar Libya Tana Ci Gaba Da Tattauna Akan Hanyoyin Shimfida Zaman Lafiya A Kasar

2020-12-07 19:33:41
Majalisar Dokokin Kasar Libya Tana Ci Gaba Da Tattauna  Akan Hanyoyin Shimfida Zaman Lafiya A Kasar

Taron da ake yi a yau Litinin a garin Gadamus dake yammacin wannan kasa share fage na wani taron da dukkanin mambobin majalisar za su halarta wanda za a bude a gobe Talata.

Daya daga cikin abinda yake jawo sabani a tsakanin ‘yan majalisar shi ne inda ya kamata a girke zauren Majalisar tsakanin birnin Tubruk ko kuma Tripoli.

Wata majiyar ta ambaci cewa; Adaidai ranar da aka tsaida cewa za a yi taron da zai kunshi dukkanin mamabobin majalisun Tubruk da na Tripoli ne, majalisar gwmanati mai matsuguni a Tripoli ta gayyaci mambobinta kadai.

Wannan sabanin dai yana zuwa ne a daidai lokacin da mayakan Halifa Haftar su ka kai hari a garin Ubari da ke kudancin kasar, da hakan wani Karin kawo cikas ne akan kokadin samun hadin kai tsakanin bangarorin biyu.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!