Ministan Harkokin Wajen Siriya Na Ziyara A Birnin Tehran

2020-12-07 14:59:26
Ministan Harkokin Wajen Siriya Na Ziyara A Birnin Tehran

Sabon ministan harkokin wajen kasar Siriya, Fayçal al-Meqdad, ya fara wata ziyarar aiki a nan Tehran.

A Safiyar yau Litini, ministan harkokin waken kasar ta Siriya, Fayçal al-Meqdad, ya gana da takwaransa Muhammad Jawwad Zarif, yayin kuma da ake sa ran zai gana da wasu manyan jami’an kasar ta Iran nan gaba.

Bayan ganawar ministocin biyu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa : ‘’Iran zata ci gaba da kasancewa a kusa da gwamnati da al’ummar Siriya, musamman a yaki da ta’addanci’’

Batun rikicin kasar ta Siriya, da alakar dake tsakaninsu na daga cikin batutuwan da bangarorin zasu tattaunawa.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!