Venezuela : Maduro Ya Samu Karin Karfin Iko Bayan Kwace Majalisar Dokoki

2020-12-07 14:56:04
Venezuela : Maduro Ya Samu Karin Karfin Iko Bayan Kwace Majalisar Dokoki

A Venezuela shugaban kasar Nicolas Maduro, ya kara samun karfin iko, sakamakon kwace rinjaye da majalisar dokokin kasar a zaben da ya gudana.

Kawacen dake goyan bayan shugaba Maduro, sun samu kashi 67,7% na yawan kuri’u miliyan 5,2 da aka kada.

A sakamakon data fitar hukumar zaben kasar ta (CNE), ‘yan adawan da suka shiga zaben suka samu kashi 18% na kuri’un da aka kada a jiya Lahadi.

Shugaban ‘yan adawa na kasar dake samun goyan bayan wasu kasashen yamma da Amurka, cewa da Juan Guaido, ya kauracewa zaben.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!