Ana Zaben Shugaban Kasa Gami Dana Yan Majalisar Dokoki A Ghana

2020-12-07 14:52:04
Ana Zaben Shugaban Kasa Gami Dana Yan Majalisar Dokoki A Ghana

A Ghana, ‘yan kasar sama da miliyan 17 ne ake sa ran zasu kada kuri’a a zaben shugabancin kasar gami dana ‘yan majalisar dokoki a yau.

‘Yan takara 12 ne ke fafatawa a zaben shugabancin kasar da suka hada da mata uku.

Takarar zaben shugabancin kasar dai zatayi zafi tsakanin dan takarar jam'iyya mai mulki ta NPP, Mr Akufo-Addo mai shekara 76, da babban abokin hamayyarsa, Mr Mahama, mai shekara 62, na jam'iyyar NDC.

Wannan dai shi ne karo na uku da ake fafatawa tsakanin tsakanin manyan ‘yan takara.

Kafain zaben dai ‘yan takaran biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar kaucewa rikicin bayan zabe a kasar da ake wa kallon misali na ingantacciyar demokuradiyya a yammacin Afrika.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!