​Najeriya: Hadiza Bala Usman Ta Ce Akwai Kalubalen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Hukumar NPA

2020-12-07 10:25:30
​Najeriya: Hadiza Bala Usman Ta Ce Akwai Kalubalen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Hukumar NPA

Shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Nijeriya NPA, Hadiza Bala Usman, ta bayyana cewa, yaki da cin hanci da kuma tabbatar da bin doka da oda shi ne babbar kalubalen da take fuskanta a gudanar da tashoshin jiragen ruwan Nijeriya.

Hajiya Hadiza ta bayyana haka ne a tattauawarta da wasu kafofin yada labarai, inda ta ce, wasu kamfanonin masu zaman kansu na amfani da wasu yarjeniyar da suka sabawa ka’idar dokoki wajen damfarar hukumar.

Ta ce, hukumar ta kalubalanci kudaden da kamfanin ‘Ocean Marine Solutions Limited ke karba da suna samar da tsaro akan jiragen ruwan da suka shigo Nieriya.

Ta kara da cewa, kamfanin ya karbi fiye da Dala Miliyan $17 a tsakanin watan Janairu zuwa Yuli na shekarar 2020 amma bai mika ko kwabo ba ga asusun gwamnatin tarayya.

“Ana samun turjiya in har ka fara yaki da cin hanci da rashawa, musamman in ka nemi cewa, hakkin kasa da na ‘yan kasa sun fi karfin wani kamfani mai zaman kansa, tare da kuma neman tabbatar da doka da oda, tabbas za ka fuskaci turjiya.


015Comments(0)
Success!
Error! Error occured!