Kasar Iran Ta ce An yi Amfani Da Makami Na Zamani Da Ake Sarrafawa Ta Tauraron Dan Adam Wajen Kashe Masanin Ilimin Nukiiyar Kasar

2020-12-06 21:17:00
Kasar  Iran Ta ce An yi Amfani Da Makami Na Zamani Da Ake Sarrafawa  Ta Tauraron Dan Adam Wajen Kashe Masanin Ilimin Nukiiyar Kasar

Kakakin dakarun kare juyin musulunci na kasar Iran Janaral Ramadan Sharif ya bayyana hakan a wajen bikin girmama masanin ilimin nukiliya kasar Muhsin Fakhrizade a lardin Hormuzgan dake kudancin kasar inda ya ce; An yi amfani da makami na zamani ne da ake sarrafashi ta hanyar Tauraron dan Adam wajen kashe masanin nukiliyar kasar a kwanakin baya.

Ya kara da cewa HKI ta sani cewa tafka irin wannan mummunan aiki na ta’adanci ba zai tafi haka nan ba tare da mayar da martani ba, domin kuwa ta shaida hakan a shekarun bayan bayan nan da suka gabata.

Daga karshe ya fadi cewa kawo tarnaki game da ci gaban da Iran take samu na fasahar nukuliya yana daga cikin babbar manufar HKI , sai dai ta sani cewa kisa baya hana Iran ci gaba da samun ilimin kimiyya na zamani, domin ta samu nasarori masu yawa a wannan bangaren albarkacin jinin shahidai , kamar yadda jagoran musulunci na Iran Ayautullah sayyid Ali Khamina’i ya jaddada game da ci gaban da kasar ta Samu na mallakar limin kimiya da fasahar zamani.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!