Kimanin Mutane 310 Ne Suka Kamu Da Cutar Korana A Cikin Kwanaki 3 A Nigeria

2020-12-06 21:09:56
Kimanin Mutane 310 Ne Suka Kamu Da Cutar Korana A Cikin Kwanaki 3 A Nigeria

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Nigeria NCDC ta bayyana cewa adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a Nigeria ya karu sosai a cikin kwanaki 3, inda aka gano mutane 310 da suka kamu da cutar a ranar Asabar da ta gabata. wannan ne ya cika adadin mutane 997 da suka kamu da cutar a tsawon sao’i 74 da suka gabata.

Tsakanin watannin Satumba da Nuwamba adadin wadanda ke kamuwa da cutar a Nigeria ya ragu sosai inda ya koma kasa da 300. Yanzu haka dai mutane 68,937 ne suka kamu da cutar a fadin kasar, yayin da mutane 1,180 kuma suka rasa rayukansu.

Babban birnin kasar Abuja ne ke kan gaba da mutane 128 sai kuma jihar Legas da mutane 86 ,sai kuma jihar Kaduna ke bi mata da mutane 26. Kimanin mutane 790,000 ne aka yi musu gwajin kamuwa da cutar acikin mutane miliyan 200 na alummar kasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!