An Kawo Karshen Yakin Neman Zabe A Kasar Ghana A Jajiberin Gudanar Da Babban Zabe A Kasar

2020-12-06 21:06:28
An Kawo Karshen Yakin Neman Zabe A Kasar  Ghana A Jajiberin Gudanar Da Babban Zabe A Kasar

Kimanin yan takara 12 ne da suka hada da mata 3 suka tsaya takarar neman kujerar shugabancin kasar ta Ghana a zaben da za’a gudanar a gobe Litinin, kuma ana ganin lamarin zai fi kamari tsakanin shugaban kasar mai ci a yanzu Nana Akufo-Addo dan shekaru 76 na jamiyar NPP da kuma tsohon shugaban kasar John Mahama na jami’yar NDC.

Biranen kasar musamman birnin Accra sun cika da hotunan yan takara da kuma hotunan tutocin jami’iyu daban daban.

A nasa bangaren babban dan takarar jami’iyar adawa ta NDC John Mahama a ranar karshe ta yakin neman zaben ya gana da sarakunan gargajiya da shuwagabannin kungiyoyin kwadago inda ya basu tabbacin samar da sabbin guraben ayyukan yi, idan har yayi nasara a zaben na gobe.

Sama da mutane miliyan 17 ne suka yi rijistar sunayensu domin kada kuri’unsu karo na 8 a zaben shugaban kasa da na yan majalisu tun bayan da kasar ta koma turbar demukuradiya kusan shekaru 30 da suka gabata.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!