An Fitar Da Kungiyar Kwallon Kafa Ta Kano Pillar Daga Gasar Zakarun Afirka

2020-12-06 21:02:47
  An Fitar Da Kungiyar Kwallon Kafa Ta Kano Pillar Daga Gasar Zakarun Afirka

A ci gaba da wasanin dake bugawa na gasar kwallon kafa ta cin kofin zakaru na “Confederation” na nahiyar Afrika an yi waje da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars daga gasar a jiya Asabar bayan da aka tashi wasan 0-0 da A.S.C Jaraaf ta kasar Senegal.

An fitar da su ne bayan da suka kasa rama cin da aka yi musu 3-1 a kasar Senigal a ranar 27 ga watan Nuwamba da ya gabata.

Ita ma kungiyar kwallon kafa ta “Plateau United” ta fice daga gasar zakarun Afrika wato “ Champions League” bayan da ta yi canjaras 0-0 da kungiyar kwallon kafa ta Simba Sports ta kasar Tanzaniya. A wasan farko da ta buga an lallasa ta da ci daya mai ban haushi. Hakazalika kungiyar kwallon kafa ta Rivers United ta sha kashi a hannun Futuro king da ci 2-1 a gida.

Yanzu haka dai kungiyar kwallon kafa ta Enyimba ce kawai ta ci wasanta na farko inda ta doke kungiyar kwallon kafa ta Rahimo da ci 1-0 a wasan da suka buga , kuma za su sake buga wasa na biyua a ranar lahadi mai zuwa.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!