​Kungiyar Kwallon Kafa Ta Al Ahli Ta Lashe Kofin Kwallon Kafa Na Masar A Karo Na 37

2020-12-06 14:57:08
​Kungiyar Kwallon Kafa Ta Al Ahli Ta Lashe Kofin Kwallon Kafa Na Masar A Karo Na 37

A wasannin cin kofin kwallon kafa na kasar Masar, kungiyar kwallon kafa ta Al ahli ta lashe kofin a karo na 37 a tarihin gasar.

An buga wasan karshe dai a daren jiya Asabar tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na Al ahli da kuma Tala’iul Jaish, inda aka tashi 3-2 bayan bugun daga kai sai mai tsaron gida, da kungiyoyin biyu suka yi kunnen doki har karshen lokacin wasan.

An sanya kwallon ta farko ne a lokacin dad an wasan Al ahli Muhammad Abdulmun’im ya jefa kwallo a ragar Tala’iul Jaish a mintuna na 65.

Sai bayan karewar mintuna 90 na wasan an shiga ‘yan mintunan da alkalin wasan yakara, inda ake shirin kammala wasan da ‘yan dakikoki, sai ‘yan wasan Tala’iul Jaish suka farke, daga nan kuma wasa ya dawo sabo.

Bayan karewa lokacin, an kara mintuna 30, daga nan kuma sai bugun dag akai sai mai tsaron gida, inda Al ahli ta samu nasarar doke Tala’iul Jaish da ci 3-2.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!