An Yi Jana’izar Matashin Bafalasdinan Da Sojojin Isra’ila Suka Kashe

2020-12-06 09:56:07
An Yi Jana’izar Matashin Bafalasdinan Da Sojojin Isra’ila Suka Kashe

A Falasdinu, a jiya Asabar ne akayi jana’izar matashin Bafalasdinan nan dan shekara 13 da ya yi shahada sakamakon harbin bindiga na sojojin yahudawan mamaya na Isra’ila a gaɓar yammacin Kogin Jordan

Daruruwan Falasdinawa suka halarci jana’izar tasa duk da halin da ake ciki na annobar korona.

A ranar Juma’a data gabata ce sojojin Isra’ilar suka harbe matashin mai suna Ali Ayman Abou Aliya, wanda ya yi shahada a gadon asibiti, inda yake jinya sakamakon shiga jikinsa da harsashi ya yi.

Kafin hakan dai dubban Falasdinawa ne ke gudanar da zanga-zanga a Gaza, domin nuna rashin amincewa da shirin Isra'ila na mamaye yankin gabar yamma da Kogin Jordan.

Masu boren na daga tutocin Falasdinawa, suna kuma yin Allah wadai da Shugaba Trump na Amurka kan goyon bayan da ya nuna ga shirin Isra'ilar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!