Ana Zaben ‘Yan Majalisar Dokoki A Venezuela

2020-12-06 09:42:39
Ana Zaben ‘Yan Majalisar Dokoki A Venezuela

Yau Lahadi ake kada kuri’a a zaben ‘yan majalisar dokoki a Venezuela, inda ‘yan takara 14,000 daga jam’iyyun siyasa 107 ke fafatawa domin samun wakilci a majalisar dokokin kasar mai kujeru 277.

Mutane miliyan 20, da dubu 700 ne ke kada kuri’a a zaben, wanda yan adawa dake rike da majalisar tun cikin 2015 suka bukaci jama’a dasu kauracewa zaben.

A nasa bangare shugaban kasar Nicolas Maduro, ya bukaci jama’a dasu fito dafifi domin kada kuri’arsu, idan suka bukatar a farfado da tatalin arzikin kasar.

Tattalin arzikin Venezuela dai ya fuskanci mummunan koma baya sakamakon jerin takunkuman Amurka.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!