Ana Samun Raguwar Masu Kamuwa Da Cutar Corona A Iran
2020-12-05 20:15:53

Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta kasar Iran ta fada a yau Asabar cewa; Wadanda su ka kamu da cutar ta corona a cikin sa’oi 24 da su ka gabata su ne dubu 12 da 151.
Mai Magana da yawun ma’aikatar kiwon
lafiya ta kasar Iran din Sima Sadat Lary, ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu jumillar adadin wadanda cutar ta kashe
tun daga bullar ta a Iran, sun kai dubu 50 da 16.
Su kuwa wadanda su ka warke daga
cutar bayan kamuwa da ita sun kai dubu 719 da 708, amma kuma abin takaici acikin sa’oi 24 da suka wuce wadanda cutar ta
kashe sun kai 321.
Wadanda kuwa aka yi gwajin a wannan
tsakanin su ne miliyan 6 da dubu dari 342 da 628.
013
Tags:
ana samun raguwar masu kamuwa da corona a iran
acikin sa’oi 24 da suka wuce wadanda cutar ta kash
sima sadat lary
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!