Jirgin Sama Maras Matuki Da Hizbullah Ta Aike Zuwa Palasdinu Da Ke Karkashin Mamaya, Ya Koma Gida Lafiya Bayan Daukar Muhimman Hotuna

2020-12-05 20:12:03

A marecen jiya juma’a ne dai kungiyar ta Hizbullah ta fitar da wasu hotuna da jirgin sama maras matuki ya dauko na wurare mafi muhimmanci a yankin Jalili da ke Plasdinu a karkashin mamaya.

Daga cikin wuraren da jirgin maras matuki ya dauko da akwai barikokin soja na ‘yan sahayoniya a jalil da kuma Shebaa.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da kungiyar gwagwarmayar ta Hizbullah take aikewa da jiragen sama marasa matuki zuwa cikin Palasdinu da ke karkashin mamaya, su kuma koma gida lafiya dauke da hotunan na cibiyoyin soja da tsaro na ‘yan sahayoniya.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!