Shugaban Kasar Ghana Akufo-Addo Ya Ce; Zai Karbi Sakamakon Zaben Shugaban Kasar Da Za A Yi A Ranar Litinin Mai Zuwa

2020-12-05 20:08:30

Shugaban kasar ta Ghna Addo Dankwa Akufo-Addo ya jaddada azamarsa ta ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, sannan kuma zai karbi sakamakon zaben a duk yadda ya zo.

A jiya juma’a ne dai shugaban kasar na Ghana ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi akan cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta 2020 wacce aka yi a Hotel din Movenpick a birnin Accra.

A ranar Litinin mai zuwa ne dai za a yi zaben shugaban kasa a kasar Ghana.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!