Sojojin Sudan Sun Kwato Yankin “Fashqah” Da Ke Karkashin Mamayar Habasha Na Tsawon Shekaru 25

2020-12-05 20:01:52
Sojojin Sudan Sun Kwato Yankin “Fashqah” Da Ke Karkashin Mamayar Habasha Na Tsawon Shekaru 25

A jiya Juma’a ne dai sojojin kasar ta Sudan su ka sanar da kwato yankin da ke kunshe da kasar noma akan iyaka da Habasha, bayan gushewar shekaru 25 yana a karkashin mamaya.

Shafin labaru na “Sudantribune” ya ambaci cewa; Sojojin na kasar Habasha sun shimfida ikonsu ne a yankin bayan da sojojin kasar ta Sudan sua ka janye a wancan lokacin.

Girman yankin na Sudan da ya sake komawa karkashin ikonta shi ne kilo mita biyar.

Tuni dai sojojin Sudan din su ka girke dakaru a wurin adaidai lokacin da sojojin na Habasha su ka mayar da hankali wajen yaki da gundumar Tigray da ya yi tawaye.

Da akwai ‘yan gudun hijirar kasar Habasha da adadinsu ya wuce 47,000 da su ka tsallaka iyaka zuwa cikin kasar Sudan.

A makon da ya shude Sudan ta mika wa Habasha sojoji 50 daga yankin Tigray da suka tsallaka iyaka.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!