Amurka Za Ta Janye Dakarunta 700 Daga Somaliya

2020-12-05 14:27:56
Amurka Za Ta Janye Dakarunta 700 Daga Somaliya

Shugaba Donald Trump, na Amurka ya bayar da umarnin janye dakarun kasarsa 700 daga kasar Somaliya, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta Pentagone, ta sanar da yammacin jiya.

Shirin janye sojojin zai somawa daga farkon watan Janairu, na shakara mai shirin kamawa gab da karshen wa’adin mulkin shugaba Trump.

Saidai Amurkar ta ce ba wai hakan yana nufi zata fice ne ba daga Afrika, zata ci gaba da kasancewa Kunlun tare da abokan huldarta a nahiyar.

Amurka dai ta ce sansanoninta na Kenya da Djibouti zasu ci gaba da gudanar da ayyukansu na yaki da ta’addanci ta hanyar jiragenta marasa direba dake kai hare hare a Somalia.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!