Manyan ‘Yan Takaran Zabe A Ghana Sun Cimma Yarjejeniyar Kaucewa Rikici

2020-12-05 14:24:13
Manyan ‘Yan Takaran Zabe A Ghana Sun Cimma Yarjejeniyar Kaucewa Rikici

Manyan ‘yan takara a zaben shugabancin kasar Ghana sun cimma matsaya kan kaucewa tada fitina bayan zaben kasar.

A jiya Juma’a ne manyan ‘yan takaran da suka hada da John Dramani Mahama da kuma shugaba mai barin Gado, Nana Akufo-Addo, suka rattaba hannun kan yarjejeniyar ta zaman lafiya.

Manufar dai ita ce kaucewa rikicin bayan zaben shugabancin kasar da zai gudana a ranar Litini mai zuwa idan Allah ya kai.

Wannan dai shi ne karo na uku da manyan ‘yan takara a zaben shugabancin kasar ta Ghana ke cimma irin wannan yarjejeniyar tun bayan shekarar 2012.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!