Gwamnatin Habasha Ta Kwace Manyan Garuruwa Daga Hannun ‘Yan Awaren Tigray

2020-11-21 14:50:22
Gwamnatin Habasha Ta Kwace Manyan Garuruwa Daga Hannun ‘Yan Awaren Tigray

Gwamnatin kasar Habasha ta sanar da cewa dakarunta sun kwace garuruwa guda biyu masu muhimmanci daga sojojin ‘yan aware na yankin Tigray na kasar a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin bangarori biyun ke ci gaba da kazanta.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce dakarun na ta sun kwace garuruwan Axum da Adwa, sannan a halin yanzu kuma dakarun na ta sun kama hanyar garin Adigrat, da ke kimanin kilomita 120 a arewacin garin Makelle, babban birnin yankin na Tigray inda dakarun suka sha alwashin sai sun kama shi.

Sanarwar ta kara da cewa: Da dama daga cikin dakarun ‘yan awaren sun mika kai lamarin da ya ba wa sojojin gwamnatin damar ci gaba da kutsawa.

Har ya zuwa yanzu dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da kama wadannan garuruwa biyun bisa la’akari da katshe hanyoyin sadarwa da gwamnatin ta yi, to sai dai an ce kama wadannan garuruwa guda biyu zai kasance lamari mai karfafa gwiwa ga dakarun gwamnatin saboda irin muhimmancin da suke da shi.

Kimanin makonni biyu kenan wannan rikici ya ke ci gaba da faruwa lamarin da ya tilasta wa dubun dubatan al’ummar yankin na Tigray yin gudun hijira zuwa kasashen makwabta musamman Sudan.

Gwamnatin firayi minista Abiy Ahmad dai tana zargin ‘yan siyasar jam’iyyar Tigray People’s Liberation Front (TPLF) da kokarin tawaye wa gwamnati ta hanyar kai hare-hare kan sansanonin sojin gwamnati da ke yankin, lamarin da gwamnatin ta ce ba za ta taba amincewa da shi ba da kuma daukar matakan ladabtar da su

014

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!