​Iran Ta Mayar Wa Manyan Kasashen Turai Da Martani Kan Batun Yarjejeniyar Nukiliya

2020-11-21 09:41:45
​Iran Ta Mayar Wa Manyan Kasashen Turai Da Martani Kan Batun Yarjejeniyar Nukiliya

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta mayar da martani dangane da wani bayani na hadin gwiwa da kasashen turai uku suka fitar kan batun yarjejeniyar nukiliya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib Zadeh ya bayyana cewa, zai fi kyau ga kasashen Jamus, Burtaniya da kuma Faransa, su yi aiki da dukkanin abin da ke ikin yarjejeniyar nukiliya da suka rattaba hannu a kanta tare da Iran, maimakon zargin Iran da kin yin aiki da wasu bangarorin yarjejeniyar.

Ya ce tun bayan da Amurka ta fice daga cikin wannan yarjejeniya tare da mayar da takunkumanta a kan Iran, wadannan kasashen turan suka yi alkawalin cewa za su ci gaba da yin aiki da yarjejeniyar, kuma za su yi aiki da wani sabon tsari na tattalin arziki tare da Iran domin kauce wa tasirin takunkumin Amurka, amma ba su yi aiki da ko daya daga cikin wadannan alkawulla da suka dauka ba.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ce, yanzu ba lokaci ne da manyan kasashen turai za su rika yin irin wannan bayani da babu lissafi a cikinsa, lokai ne da za su yi aiki da alkawullansu da suka rattaba hannu akansu.

Ya kara da cewa, sashe na 26 da 36 sun bai wa Iran damar jingine yin aiki da wani bangaren yarjejeniyar, matukar wasu daga cikin kasashen da suka rattaba hannu kanta bas u yi aiki da nasu alkawullan ba, kuma abin da Iran ta yi kenan, kuma da zaran dukkanin kasashen da suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya sun dawo suna yin aiki da ita, to ita za ta ci gaba da yin aiki da ita.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!