​Najeriya: Malaman Jami’a Sun Sulhunta Da Gwamnatin Tarayya

2020-11-21 09:25:57
​Najeriya: Malaman Jami’a Sun Sulhunta Da Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta amince da tsame malaman jami’a daga cikin ma’aikatan da za ta rika biya a karkashin tsarin albashi na bai-daya.

Jaridar Daily Trust ta bayar da rahoton cewa, a tattaunawar sulhuntawa da kungiyar malaman jami’a ta ASUU, gwamnati ta amince ta biya su albashin watan Fabrairu zuwa Yuni da suke binta bashi.

Da yake magana bayan tattaunawarsu ta kusan awa bakwai, Ministan Kwadago Chris Ngige ya ce, gwamnatin ta amince da yawan kudaden da za ta ba malaman daga Naira biliyan 50 zuwa biliyan N60.

Ya ce an kara yawan alawus dinsu daga biliyan N30 zuwa biliyan N35 sai kuma kudaden gyare-gyare da aka kara zuwa biliyan N25 daga Naira biliyan 20.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!