​Sakataren Kungiyar Kasashen Larabawa Ya Yi Allawadai Da Ziyarar Pompeo

2020-11-21 09:20:38
​Sakataren Kungiyar Kasashen Larabawa Ya Yi Allawadai Da Ziyarar Pompeo
Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa Ahamd Abul Ghiaz ya yi Allawadai da ziyarar da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya kai a cikin yankunan Falastinawa da Isra’ila ta mamaye da kuma Tuddan Golan na Syria.

Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa Ahamd Abul Ghiaz ya bayyana cewa, wannan ziyara da Pompeo a cikin yankin Golan na Syria da yahudawan Isra’ila suka mamaye abin Allawadai ne, kuma hakan ba zai taba halasta wa Isra’ila mallakar tuddan Golan na kasar Syria ba.

Ya kirayi gwamnatin Amurka da ta kawo karshen irin wannan aiki na tsokana wanda ya yi hannun riga da dukkanin dokokin kasa da kasa, domin kuwa bisa dokokin majalisar dinkin duniya, Tuddan Golan mallakin kasar Syria ne, kuma mamamyar da Isra’ila take yi wa wannan yankin ba hakastacciya ba ce bisa dokokin duniya.

Gwamnatin Falastinawa a nata bangaren, bayan yin tir da ziyara da Mike Pompeo ya kai matsugunnin yahudawa na Jabal Tawil da ke cikin yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye , kuma tuddan Golan na Syria wanda shi ma Isra’ila take mamaye da shi, gwamnatin Falastinawa ta bayyana wannan mataki da cewa na tsokana ne.

A nata bangaren gwamnatin kasar Syria ta bayyana cewa, wannan mataki bai zo mata da mamaki ba, domin kuwa babban abin da gwamnatin Trump ta aiwatar baki daya a cikin shekaru hudu, shi ne mara baya ga ayyukan ta’addancin Isra’ila a kan al’ummomin yankin.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!