Wata Kungiyar Gwagwarmaya Ta Kasar Iraki Ta Ce; Tsagaita Wutar Yaki Tsakaninta Da Amurka Ya Zo Karshe

2020-11-20 14:04:57
Wata Kungiyar  Gwagwarmaya Ta Kasar Iraki Ta Ce; Tsagaita Wutar Yaki Tsakaninta Da Amurka Ya Zo Karshe

Kungiyar gwgawarmayar ta Iraki mai suna; “Asa’ib Ahlul-Haqq’ ta bakin shugabanta, Sheikh Qais Khaza’ali ce ta sanar da kawo karshen tsagaita wutar yakin bisa sharadin da ‘yan gwagwarmaya su ka kafa.

Qais Khaza’ali ya shaidawa tashar talabijin din al’alam ta Iran a wata hira da shi, ya ce gwagwarmaya za ta ci gaba da kai hare-harenta, bisa la’kari da yanayin da ake ciki a yanzu.

Khaazali ya kuma ce; Manufa daya ce ta sa kungiyoyin gwgawarmaya su ka dauki makami, idan wannan dalilin ya kau, to su ma za su ajiye makamansu.

Shugaban kungiyar kungiyar ta gwgawarmaya a kasar Irakin ya kara da cewa; Tsarin mulkin kasar Iraki bai bayar da dama ga sojojin kasashen waje su kafa sansanoni a cikin kasar ba, sai idan majalisar dokoki ta amince.

Har ila yau Khaza’ali ya yi kira da a yi aiki da dokokin kasar Iraki akan laifukan da sojojin Amurka suke tafkawa a cikin kasar.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!