Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya Ya Kore Zargin Da Gwamnatin Habasha Ta Yi Masa Na Taimaka Wa “Yan Awaren Tigray

2020-11-20 14:02:01
Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya  Ya Kore Zargin Da Gwamnatin Habasha Ta Yi Masa Na Taimaka Wa “Yan Awaren Tigray

Shugaban hukumar lafiya ta duniya ( WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus wanda dan asalin yankin ne na Tigray, ya karyata zargin da sojojin Habasha su ka yi masa na cewa yana taimakawa ‘yan awaren.

A jiya Alhamis ne dai Habasha ta sanar da cewa; sojojinta sun sami nasarori akan ‘yan awaren na yankin Tigray saboda sun karaci birnin Mekelle da shi ne babban birnin yankin.

Adhanom Ghebreyesus ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; “ Wasu rahotanni suna zargina da taimakawa wani gefe daya a halin da ake ciki. To wannan ba gaskiya ba ne,abinda kawai zan iya fada shi ne ina tare da zaman lafiya.”

Shugaban hukumar Lafiyar ta duniya ya kara da cewa:
Zuciyata ta karaya matuka saboda abinda yake faruwa a kasata Habasha, don haka ina yin kira ga dukkanin bangarorin da su yi aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya da kuma tabbatar da kare lafiyar fararen hula.

Habasha Ta Zargi Shugaban WHO Da Taimakawa ‘Yan Tawayen Tigray Na kasar

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!