Karamin Jakadan Kasar Faransa A Moroko Ya Kashe Kansa

2020-11-20 13:55:14
Karamin Jakadan Kasar Faransa A Moroko Ya Kashe Kansa

An sami gawar karamin jakadan na Faransa ne Donius Fransua a jiya Alhamis a cikin dakinsa a jikin igiyar rataye kai tana lilo.

Kafafen watsa labarun kasar Moroko sun ambaci cewa; bayan abinda ya faru a garin Danja da ke arewacin kasar jami’an tsaro sun shiga halin ko-ta-kwana.

Karamin jakadan na Faransa dan shekaru 55 ya rataye kansa ne da igiya a cikin dakinsa a garin Danja da nan ne karamin ofishin jakadancin Faransa yake.

Gabanin kashe kan nasa dai, Fransua ya gabatar da takardar neman barin aiki saboda matsaloli na kashin kai da ya ce yana fuskanta, makwanni kadan bayan nada shi akan mukanin nashi.

Tuni dai Faransa ta bude bincike domin gano musabbabin kashe kai da karamin jakadan nata ya yi.

A cikin watan Satumba na wannan shekarar ne dai aka nada Donius Fransau a matsayin karamin jakadan kasar Faransa a birnin Danja da ke kasar ta Moroco.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!