Mutane 16 Sun Mutu Sakamakon Zanga-Zangar Kama Dan Takarar Shugaban Kasa A Uganda

2020-11-19 21:33:14
Mutane 16 Sun Mutu Sakamakon Zanga-Zangar Kama Dan Takarar Shugaban Kasa A Uganda

Rahotanni daga kasar Uganda sun bayyana cewar wasu mutane 16 sun rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar da ta barke biyo bayan kama daya daga cikin ‘yan takaran shugabancin kasar, Robert Kyagulanyi da aka fi sani da Bobi Wine, da jami’an tsaro suka yi.

A jiya Laraba ne dai jami’an tsaro suka kama Bobi Wine din a gabashin kasar Ugandan saboda zargin da suke masa na keta dokokin zabe da suka bukaci ‘yan takara da kada su gudanar da wani taron neman zaben da ya wuce na mutane 200 saboda dakile yaduwar cutar nan ta COVID-19.

Rahotanni dai sun ce zanga-zangogi sun barke a sassa daban-daban na kasar bayan da magoya bayansa suka sami labarin kama shi da kuma tsare shi da jami’an tsaron suka yi, lamarin da yayi sanadiyyar fito-na-fito da masu zanga-zangar suka yi da ‘yan sandan abin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai da kuma ranana wasu sama da 40.

A wata sanarwa da ta fitar Kungiyar Red Cross ta kasar Ugandan ta ce ma’aikatanta da suke fage sun ba wa wasu mutane da aka kawo su da harbin bindiga su 11 magani a sansanoninsu.

Tuni dai wasu daga cikin ‘yan takaran shugabancin kasar Ugandan suka dakatar da yakin neman zaben da suke yi don nuna rashin amincewa da abin da ke faruwar da kuma kiran ‘yan sandan da su daina amfani da karfi kan masu zangar lumana a kasar.

A halin yanzu dai ana ganin Bobi Wine wanda mawaki ne kuma dan shekaru 38 a duniya, ana ganinsa a matsayin wani dan siyasa matashi mai tasiri cikin siyasar kasar, kana kuma barazana ga shugaban Yuwei Museveni na kasar.

014

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!