Habasha Ta Zargi Shugaban WHO Da Taimakawa ‘Yan Tawayen Tigray Na kasar

2020-11-19 21:23:13
Habasha Ta Zargi Shugaban WHO Da Taimakawa ‘Yan Tawayen Tigray Na kasar

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Habasha Berhanu Jula ya zargin babban daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Ghebreyesus da goyon bayan ‘yan tawayen yankin Tigray da nema mausu hanyoyin samun makamai.

Rahotanni daga kasar Habashan sun jiyo hafsan hafsoshin sojin yana fadin cewa babban daraktan WHO din wani kusa ne a jam’iyyar TPLF mai rike da yankin na Tigray don haka ba ya kasa a gwiwa wajen taimakon ‘yan tawayen na Tigray.

Mr. Tedros Ghebreyesus shi ne jami'in cibiyar kasa da kasa mafi girma wanda ya fito daga yankin na Tigray.

Rikici dai ya barke kasashen dakarun gwamnatin Tarayyar Habashan da na yankin Tigray din ne bayan da ya zargi gwamnatin yankin da yin zagon kasa ga gwamnatinsa bayan da sojojin yankin suka kai hari wasu sansanonin sojin gwamnatin tarayyar da suke yankin na Tigray hari da kuma kwashe makamai lamarin da ya haifar da yakin da ya zuwa yanzu aka dau kimanin makonni uku ana yinsa da yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa da kuma raunana wasu da adadi mai yawa bugu da kari kan tilasta wa wasu dubbai gudun hijira.

Har ya zuwa yanzu dai babban darajan WHO din bai ce komai kan wannan zargi da ake masa ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!