Rahotanni: Daga 2014 Zuwa Yanzu Amurka Ta Kashe Fararen Hula 13,000 A Kasashen Iraki Da Siriya

2020-11-19 21:20:25
Rahotanni: Daga 2014 Zuwa Yanzu Amurka Ta Kashe Fararen Hula 13,000 A Kasashen Iraki Da Siriya

Cibiyar nan ta Airwars, mai sanya ido kan lamurran da suka shafi yaki, ta bayyana cewar tsawon shekaru shidan da suka gabata, sojojin Amurka sun kashe fararen hula sama da 13,000 a kasashen Iraki da Siriya biyo bayan hare-haren da suka kai kasar.

Cibiyar ta bayyana cewar ta samo wannan bayanin ne cikin wasu bayanan da ta samo daga cibiyoyin sojin Amurkan da ke nuni da irin hare-haren da sojojin Amurkan suka kai wadannan kasashen tun daga shekara ta 2014 bayan da Amurkan ta kaddamar da abin da ta kira fada da ta’addanci a wadannan kasashen biyu.

Cibiyar ta jiyo tsohon kakakin rundunar hadaka da Amurkan take wa jagoranci Myles Caggins yana tabbatar da wadannan bayanan inda ya ce sun fitar da su ne don tabbatarwa da duniya cewa su ba sa son nuku-nuku.

Bayanan dai sun yi nuni ne da irin hare-haren da Amurkan ta dinga kai wa wajaje daban-daban na wadannan kasashen lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawan gaske na fararen hula da ba su ci ba su sha ba.

An jima dai ana zargin sojojin Amurka da kai hare-hare wajajen fararen hula da kashe wani adadi na mutanen da suke wajen ba gaira babu dalili a kasashen Iraki da Siriyan.

014

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!