Kasar China Ta Kirayi Amurka Da Ta Koma Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya Ta Iran

2020-11-19 13:41:15
Kasar China Ta Kirayi Amurka Da Ta Koma Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya Ta Iran

Wakilin din-din din na kasar China a Hukumar makamashin Nukiliya Ta MDD, Wang Wen ne ya yi wa Amurka wannan kiran na ta koma aiki da yarjejeniyar Nukiliya ta Iran sannan kuma ta yi watsi da matsin lambar da take yi wa Iran ta fuskar tattalin arziki.

Radiyon kasar Sin na kasa da kasa ya ambato wakilin kasar a hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa yana cewa; Ficewar da Amurkan ta yi daga cikin yarjejeniyar ita kadai, da kuma yi wa Iran matsin lamba, wani abu ne da duniya ba ta amince da shi ba.

Har ila yau Wang ya jaddada cewa; Aiki da hanyoyin diplomasiyya shi ne komawa aiki da yarjejeniyar ta Nukiliya.

Matakin na Amurka dai yana cin karo da kudurin MDD mai lamba 2231 akan yarjejeniyar ta Nukiliya da Iran.

Kasashen China da Rasha, ba su aiki da takunkuman Amurka akan Iran, sabanin sauran kasashen turai da su ke cikin yarjejeniyar ta Nukiliya.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!