FIFA Ta Dauki Alkalan Kwallon Kafa Uku Daga Iran Saboda Wasannin Shekara Ta 2021 Mai Zuwa

2020-11-19 13:38:24
FIFA Ta Dauki Alkalan Kwallon Kafa Uku Daga Iran Saboda Wasannin Shekara Ta 2021 Mai Zuwa

Shugaban hukumar kwallon kafa a yammacin Iran, Abbas Sufy ne ya sanar da cewa FIFA din ta zabi Payam Haidari da Bijin Haidari a cikin alkalan kwallon kafa da za su yi ma ta aiki a shekarar wasanni ta 2021.

Sai kuma mataimakiyar alkalin wasannin kwallon kafa wacce ita ce ta uku da aka dauka daga Iran, wato Baharah Saify.

Dukkanin alkalan su uku dai suna da wkarewar da za su iya yin alkalanci a wasannin duniya.

Biyu daga cikin wadanda aka zaba din sun yi aiki tare da hukumar ta FIFA tun a shekarar 2016.

013


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!