Kakakin Sojan Yemen Ya Ce: Bangaren Farko Na Musayar Fursunoni Ya Kammala Cikin Nasara

2020-10-17 11:45:54
Kakakin Sojan Yemen Ya Ce: Bangaren Farko Na Musayar Fursunoni Ya Kammala Cikin Nasara

Janar Yahya Sari’i, wanda shi ne mai Magana da yawun sojojin kasar Yemen, ya fadawa tashar talabijin din ‘almasirah’ cewa; Musayar fursunonin da aka yi da abokan gaba, babbar nasara ce ta fuskokin ‘yanadamtaka, da siyasa da kuma soja.

Janar Sari’i ya ci gaba da cewa; Wasu daga cikin fursunonin da aka yi musayar su sun yi zaman kusan shekaru 5 a gidajen kurkuku, yana kuma mai cewa; Mun kasance muna kula da fursunonin abokan gaba sosai, akasin yadda su ka kula da fursunonin namu.

A shekaran jiya Alhamis ne dai aka yi musayar fursunoni a tsakanin kasar Yemen da kuma kawancen Saudiyya na yaki, inda fursunonin na Yemen su ka sauka a filin saukar jiragen sama na birnin San’a.

Sai dai janar Yahya Sari’i, ya tabbatar da cewa a shirye su ke anan gaba su yi wata musayar fursunonin da abokan gaba.


013

Comments(0)