An Bude Yakin Neman Zabe A Kasar Cote De Voire A cikin Tashe-tashen Hankula

2020-10-17 11:42:10
An Bude Yakin Neman Zabe A Kasar Cote De Voire A cikin Tashe-tashen Hankula

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka bude yakin neman zaben shugaban kasar wanda za a gudanar a ranar 31 ga watan nan na Oktoba.

Sai dai yakin neman zaben yana tattare da rikice-rikice na masu nuna adawa da tazarcen shugaba Alassane Outtara a karo na uku.

A makon da ya gabata masu Zanga-zangar a birnin Abidjan sun rika bayar da taken cewa; Ba su yarda da sake tsayawa takarar Outtara karo na uku ba.

Da akwai ‘yan takara uku da za su kara da shugaba mai ci Alassan Outtara da su ne: tsohon shugaban kasar Henri Konan Bedie, Pascal Affi N’ Guessan, sai kuma tsohon dan majalisa, Kouadio Konan Bertin.

Kotun tsarin mulkin kasar ta yi watsi da ‘yan takara 40 da su ka hada da tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo dan shekaru 75, da kuma tsohon dan tawaye, Guillaume Soro dan shekaru 47.


013

Comments(0)