Gwamnatin Tarayyar Nigeria Ta Fara Raba Kayan Agaji Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Rusta Da Su A Jihar Sokoto

2020-10-17 11:38:32
Gwamnatin Tarayyar Nigeria Ta Fara Raba Kayan Agaji Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Rusta Da Su A Jihar Sokoto

A jiya Juma’a ne dai ministar ayyukan jin kai ta kasar Nigeria, Hajiya Saadiya Umar ta sanar ta cewa; An fara gudanar da ayyukan bayar da taimakon ne bisa umarnin shugaba Muhammadu Buhari domin saukakawa mutane asarar da su ka yi.”

Minista Sa’adiyya ta kara da cewa; “Mun zo nan ne domin zartar da aiki mai muhimmanci bisa umarnin shugaba Muhammadu Buhari domin tausayawa mutane da gwamnatin Sokoto saboda ambaliyar ruwar da ta faru a cikin wasu yankuna na jihar.

Har ila yau, ministar ta ci gaba da cewa; A yau muna yin abubuwa guda biyu ne, da su ne; Raba wa wadanda ambaliyar ruwan ta rutsa da su karya kayan agaji, da kuma rabawa matan karkara naira dubu 20-20.

Jihohin Sokoto da Kebbi suna daga cikin yankunan da su ka fuskanci ambaliyar ruwa ba.

013

Comments(0)