Iran Ta Zama Kasa Ta Farko Wajen Kiwon Kifin Salamone A Duniya

2020-09-15 21:33:54
Iran Ta Zama Kasa Ta Farko Wajen Kiwon Kifin Salamone A Duniya

Shugaban albarkatun kifi na Iran, Khan Mirzai ne ya sanar da cewa kasar Iran din ta zama ta farko a fagen kiwon kifin Salamone, sannan kuma ta biyu wajen samar da kwan kifin Caviar.

Khan Mirzai ya kuma bayyana cewa; Yawan kifaye da kuma albarkatun ruwan da Iran din take samarwa ya karu sosai, ta yadda a fagen samar da ‘jatanlande’ take ta goma a duniya.

A farkon juyin musulunci Iran tana samar da albarkatun ruwan ne da basu wuce ton dubu 32 ba,amma a yanzu ta zama wacce ta wadatu daga shigo da albarkatun ruwa daga waje.


013

Comments(0)