Shugabannin ECOWAS Sun Sake Ganawa Da Sojojin Mali

2020-09-15 21:29:34
Shugabannin ECOWAS Sun Sake Ganawa Da Sojojin Mali

A yau Talata ne dai wa’adin da kungiyar tattalin arzikin ta yammacin Afirka ta shatawa sojoji masu mulki a kasar Mali na su fitar da farar hular da zai yi mulki ya zo karshe.

Bugu da kari shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afirka din suna son wa’adin da za a yi mulkin rikon kwarya ka da ya wuce shekara daya.

Shugabannin kungiyar tattalin arzikin ta yammacin Afirka ta kasashe 15, sun taru a kasar Ghana a karkashin sabon shugabanta Nana Akufo-Addo.

Su dai sojojin na Mali su na son wa’adin rikon kwaryar ya dauki watanni 18, kuma shugaban gwamnatin zai iya zama soja.

A ranar 18 ga watan Ogusta ne dai sojojin kasar ta Mali su ka kifar da gwamnatin shugaba Bubakar Keita.


013

Tags: juyin mulki
Comments(0)