Washington Post : Shirin Trump A Gabas Ta Tsakiya, Kawalwalniya Ce

2020-09-15 21:26:40
Washington Post : Shirin Trump A Gabas Ta Tsakiya, Kawalwalniya Ce

A wata kasida da jaridar ta buga ta bayyana cewa; Babu alamar da ke nuni da salon sulhu da zaman lafiyar da Paalsdinawa za su samu a karkashin mamayar Isra’ila, a yayin da kasashen larabawan takun pasha su ke karbar jakadun Isra’ila.

A yau Talata ne za a rattaba hannu akan yarjejeniyar kulla alaka a tsakanin kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain a gefe daya, da kuma Haramtacciyar Kasar Isra’ila a daya gefen, a kasar Amurka.

Wani sashe na kasidar ta jaridar Washingtong Post ya kunshi cewa; A cikin gida Donald Trump yana tsorata al’ummar kasar, yayin da a waje yake nuna cewa yana son sulhunta kasashe.

Kasidar ta ci gaba da cewa; shugaban na kasar Amurka yana son wani abu da zai rike domin yin yakin neman zabe.

Daga cikin mahalarta taron rattaba hannu akan yarjejeniyar a yau a fadar mulki ta Amurka “ White House” da akwai Fira ministan HKI, Benjamin Netanyahu, sai kuma jami’an gwamnatocin kasashen Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa.


013

Tags: donald trump
Comments(0)