​Zarif: Trump Ya Sanya Larabawa Kulla Alaka Da Isra’ila Ne Domin Daukar Hoton Takarar Zabe

2020-09-15 14:32:26
​Zarif: Trump Ya Sanya Larabawa Kulla Alaka Da Isra’ila Ne Domin Daukar Hoton Takarar Zabe

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, babbar manufar shugaban kasar Donald Trump ta tilasta wasu kasashen larabawa da su kulla alaka da Isra’ila ita ce daukar hoton da zai nuna domin yakin neman zabe.

Tashar Press TV ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayaninsa da ya saka a shafinsa na twitter, Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, Donald Trump na neman hoton saka wa ne domin yakin neman zabe da ke karatowa a Amurka, a kan haka ya sanya surukinsa Jared Kushiner ya tilasta wasu daga cikin sarakunan larabawa masu yi masa biyayya sau da kafa kan su gaggauta sanar da kulla alaka da Isra’ila.

Zarif ya ce ko shakka babu, manufar hakan ita ce daukar hoto tsakanin wadannan sarakunan larabawa tare da Netanyahu da kuma Trump, inda Trump da Netanyahu dukakninsu za su amfani da wadannan hotuna domin cimma manufofinsu na siyasa, musamman a daidai lokacin da suke ci gaba da rasa magoya baya.

Ya kara da cewa, sarakunan larabawan da suka mika kai ga wannan manufa ta Trump za su jawo wa kansu fushin al’ummominsu domin dada wa Trump da Netanyahu, wanda hakan babban abin kunya ne

Tags:
Comments(0)