Kasar Benin Tana Bikin Cika Shekaru 60 Da Samun “Yancin Kai

2020-07-31 21:06:39

Kasar Benin da ke yammacin Afirka tana bikin cika shekaru 60 da samun ‘yanci daga ‘yan mulkin mallakar Faransa

Kasar ta Benin, wacce a yayin samun ‘yancinta aka santa da sunan; “Jamhuriyar Dahomey” ta fuskanci rikice-rikice na siyasa a shekaru 10 na farkon samun ‘yancin nata wanda a wasu lokutan ya hada tashe-tashen hankula.

Ana sa ran cewa za a gudanar da bukukuwa na zagayowar ranar samun ‘yancin, sai dai saboda cutar corona ba za a yi manyan takura ba ko rawar daji da sojoji a manyan filayen tarukan kasar.

Rahotanni da suke fitowa daga babban birnin kasar Cotonou na nuni da cewa ya zuwa yanzu babu wasu alamu da suke nuni da kawata titunan da tutocin kasar kamar yadda aka saba akowace shekara.


Tags:
Comments(0)