Daliban Iran 4 Sun Sami Kyautukan Kasa Da Kasa Na Olympia A Fagen Ilimin Kimiyya

2020-07-31 21:01:50

Daliban na Iran sun sami kyautunan yabo na zinariya biyu, sai kuna na azrufa biyu da tagulla guda a wurin gasar Olympia ta kasa da kasa ta kimiyya karo na 52.

Fagegen da ake gudanar da gasar a cikinsu sun kunshi lissafi, da kimiyyar lissafi da kuma kimiyyar sanadarori. Sai kuma ilimomin sararin samaniya da kwamfuta, sannan kimiyyar halittu.

Dalibai ne daga makarantu daban-daban na duniya su ke shiga gasar ta ilimi domin fitar da masu baiwa da gwanaye.

Fiye da shekaru 40 kenan da daliban Iran su ke shiga cikin irin wannan gasa ta ilimi ta kasa da kasa.

Tags:
Comments(0)