Siriya: Gwamnati Da Mutanen Kasa Za su Daurewa Takunkuman Amurka

2020-06-29 14:53:05

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Siriya Faisal Miqdad ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta Siriya tare da mutanen kasar za su ci gaba da dauriya da kuma fuskantar takunkuman kasar Amurka kamar yadda suka daure da makirce-makircenta shekaru 10 da suka gabata.

Mikdad ya kara da cewa sabbin takunkuman tattalin arzikin da gwamnatin kasar ta Amurka ta dorawa kasar sun shafi hatta makwabtan kasar da kuma kawayenta, don haka gwamnatin kasar za ta yi aiki tare da wadannan kasashe don ganin takunkuman ba su yi tasirin a zo a ga ni ba.

A makon da ya gabata ne Amurka ta dorawa gwamnatin kasar Siriya takunkuman tattalin arziki masu tsanani don hana shirin sake gina kasar tafiya.

Takunkuman wadanda ake kira “Kanunu Kaisar” ko dokokin Caesar, suna nufin killace kasar Siriya daga kasashen duniya gaba daya, har zuwa lokacin da za ta mika kai ga bukatun Amurka da Isra’ila.

Tags:
Comments(0)