An Kama ‘Yan Ta’addan Daesh 14 A Iraki

2020-06-29 14:50:12

Gwamnatin kasar Iraki ta bada sanarwan cewa jami’an tsaron kasar sun sami nasarar kama ‘yan ta’adda ‘yan kungiyar Daesh 14 a lardunan Kirkuk da kuma Salahuddin a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan al’amuran cikin gida yana fadar haka a safiyar yau Litinin. Ministan ya ce, duk da cewa babu wani yankin kasar Iraqi a karkashin ikon kungiyar, amma har yanzun akwai wasu ‘ya’yanta wadanda suke kai hare-hare sari ka noke daga lokaci zuwa lokaci a cikin kasar.

A shekara ta 2014 ne kungiyar Daesh karkashin Abubakar Badgadi sun mamaye yankunan arewacin kasar Iraki da dama, tare da taimakon kasashen yamma da kuma wasu kasashen yankin, wadanda suka hada da kasar Saudiyya.

Kungiyar ta aikata kisan kiyashi ga dubban mutanen kasar a cikin lokacin da suke iko da yankunan arewacin kasar. A shekara 2017 ne gwamnatin kasar Iraqi tare da taimakon JMI ta kwace iko da dukkanin yankunan da kungiyar ta mamaye a kasar.

Tags:
Comments(0)