Libya: Dakarun Haftar Sun Kai Hari Kan Dakarun Gwamnatin Tripoli

2020-06-29 14:49:00

Majiyar sojojin Halifa Haftar a kasar Libya ta bayyana cewa jiragen yakin sun kai hare-hare ta sama a kan wasu wurare a kusa da birnin Misrata daga yammacin kasar.

Rundunar sojojin na halifar Haftar ta kara da cewa jiragen saun sami nasarar lalata sansanonin sojojin gwamnatin Tripoli kimanin 30 sanadiyyar hakan.

Shafin facebook na sojojin Halifa Haftar da ke birnin Bangazi daga gabacin kasar ya kara da cewa jiragen sun cilla makamai masu linzami kan garuruwa da dama a gewayen birnin na misrata a safiyar yau Litinin.

A cikin yan makwannin da suka gabata ne sojojin gwamnatin Tripoli suka sami nasarar korar sojojin Haftar daga yankunan da dama a kusa da birnin Tripoli babban birnin kasar.

Kasashen Masar da kuma Faransa na daga cikin wadanda suke goyon bayan Haftar a kokarin da yake na kwace iko da kasar Libya gaba daya. A yayin da gwamnatin kasar Turkiya da wasu kasashen Larabawa suka goyon bayan gwamnatin Tripoli wacce Fa’iz Sarraja yake jagoranta.

Tags:
Comments(0)