Ranar Quds Ta Duniya

2020-05-21 22:46:41

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, zai yi wa musulmin duniya jawabi a wannan Juma’ar kan ranar Quds ta duniya.

Za'a watsa jawabin ne kai tsaye ta gidajen radiyo da talabijin na Iran.

A shekarun baya dai akan gudanar jerin gwano ne na nuna goyan bayan al’ummar Falasdinu, saidai a bana ba za’a gudanar da jerin gwanon ba kamar yadda aka saba saboda annobar korona data addabi duniya.

A Iran an takaita tarukan a masallatai da kuma cibiyoyin ilimi a biranan da ba su fuskantar wata barazana ta a zo gani dangane da cutar corona.

Ana dai gudanar da ranar ta Quds ne a ko wacce Juma’ar karshe ta watan Ramadana, kamar yadda mirigayi Iman Khomeiny, wanda ya asasa jamhuriyar musulinci ta Iran, ya ayyana ta a matsayin ranar tunawa da masallacin Quds da kuma zalincin yahudawan mamaya na Isra’ila kan al’ummar Palasdinu.

Tags:
Comments(0)