​Janar Hatami: Amurka Za ta Fuskancin Martani Idan Ta Taba Jirgin Man Iran

2020-05-21 17:01:54

Ministan tsaro na kasar Iran Brigadier General Amir Hatami ya fadi cewa; yana gargadin Amurka da ta daina duk wani aikin tsokana a kan katafaren jirgin rowan Iran na dakon mai, wanda yake tafiya a halin yanzu a cikin ruwa na kasa da kasa zuwa kasar Venezuela.

Janar Hatami ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake mayar da martani game da tsokanar da Amurka take yi dangane da jirgin rowan na Iran mai dauke da tataccen man fetur.

Ya ci gaba da cewa Amurka ba ta da hakki na mayar da kanta ‘yar sanda a kan dukiyoyi da kaddarorin kasashen duniya a cikin ruwa na kasa da kasa, domin dokokin duniya da aka amince da su, sun baiwa kowace kasa ta duniya damar yin amfani da ruwa na kasa domin harkokinsu na kasuwanci da makamantan hakan, kamar yadda ita ma Amurka take yi.

A baya-bayan ne wani jami’an gwamnatin Amurka ya bayyana cewa, suna duba yiwuwar daukar mataki kan jiran man na kasar Iran da ke hanyarsa ta zuwa kasar Venezuela dauke da tataccen man fetur.


Tags:
Comments(0)